1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hasashe kan zaɓen 'yan majalisa a Libiya

Usman ShehuJuly 6, 2012

Masana sun bayyana irin ƙalubalen dake gaban 'yan majalisar dokoki da za a zaɓa a ƙasar Libiya, wadda ke fama da rikici

https://p.dw.com/p/15T23
Libyen vor den ersten demokratischen Wahlen. Libya is moving towards elections provided for the first time. Libyan girls are recorded at the headquarters of the elections and by women who were Tahlihn in courses on the electoral process Foto: Essam Zouber, DW arabisch Korrespondentin in Libyen. Place and Date : Tripoli – Libya 6-6 -2012
Bildergalerie Libyen vor den ersten demokratischen WahlenHoto: DW

A wannan Asabar ce al'ummar ƙasar Libiya ke zuwa runfunan zaɓen majalisar da za ta shatawa ƙasar kundin tsarin mulki a dai dai lokacin da matsalar taɓarɓarewar lamuran tsaro ke ci gaba da addabar ƙasar.

Kimanin watanni tara kenan bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaban Libiya Mu'ammar Gaddafi, al'ummar ƙasar ke fuskantar wani sabon yanayi a tarihin rayuwar su, domin cikin kimanin shekaru 40 da Gaddafin ya yi akan mulkin ƙasar ba ta da majalisar dokoki ko tsarin mulki, inda zama wakilin wata jam'iyyar siyasa ma ka iya sanya mutum fuskantar hukuncin kisa. Sai dai kuma a karon farko cikin kusan ƙarni guda al'ummar Libiya za ta ɗanɗana abin da za'a kira zaɓe, kana galibin mutane miliyan biyu da dubu 800 da aka yiwa rajista za su jefa ƙuri'a a karon farko cikin rayuwar su.

Abir Berhim (l), mit Tinte am Finger als Zeichen zur Beteiligung an der Wahl, wirft am Dienstag (03.07.2012) im Wahllokal in Berlin seinen Stimmzettel in die Wahlurne. Die Wahl des libyschen Nationalkongresses ist in Deutschland verhalten angelaufen. Am ersten von fünf Wahltagen sei die Beteiligung der Exil-Libyer bis zum Nachmittag eher gering gewesen, sagte der Berater der Wahlkommission Libyens in Deutschland, Graibei, am Dienstag in Berlin. Foto: Claudia Levetzow/lbn (zu lbn 1006 vom 03.07.2012)
Wasu yan Libiya ke kada kuri'aHoto: picture alliance / dpa

Sai dai kuma zaɓen wakilan majalisar dokoki 200 da za su tsarawa ƙasar sabon tsarin mulki game da kafa gwamnati na zuwa ne a yayin da ƙasar ke fama da ƙalubalen tsaro a sassa daban daban, wanda ma ya kai ga ƙona wasu ofisoshin ita kanta hukumar zaɓen da ma takardun zaɓen da za'a yi anfani da su a ranar Asabar dake tafe, amma duk da haka majalisar wucin gadin ƙasar ta Libiya ta ce babu abinda zai hana ta gudanar da zaɓen.

Faɗan da ake gwabzawa tsakanin 'yan ƙabilar Tubawa da kuma Zwai a garin Kufra dake yankin kudancin ƙasar ta Libiya ya janyo mutuwar kimanin mutane 250, kamar yadda wani matashi mai suna Youssef daga ƙabilar Walid Sulaiman dake birnin Sabha ke faɗi:

"Ya ce suna kashe mutane, suna satar motoci suna haddasa mana fitintinu da yawa. Duk Tubawa ne baƙi waɗanda ba su da takardu ke yin haka."

Sai dai kuma wani Ba-Tube, mai suna Youssef Sidi Barka da shi ma ke zaune a birnin na Sabha inda kimanin mutane 150 suka mutu a baya-bayannan cewa ya yi 'yan ƙabilar sa ne ke fuskantar hare-hare daga mayaƙan sa kai:

Milizionäre kontrollieren am Montag (04.06.2012) an einem Checkpoint in Tripolis Fahrzeuge. Bewaffnete haben den Flughafen in der libyschen Hauptstadt Tripolis gestürmt und kurzzeitig den Betrieb lahmgelegt. Foto: Hannibal dpa
Wuraren bincike a birnin TiripoliHoto: picture-alliance/dpa

" Ya ce yaƙi ne irin na basasa. Ƙungiyoyin sa-kai ne na Larabawa suka kawo mana hari a unguwar Tubawa. Mu Tubawa bamu kaiwa kowa hari ba. "

Hatta baƙin da suka zo ƙasar ta Libiya domin neman abinci dai ba su tsira daga faɗace-faɗacen dake ci gaba da wanzuwa a tsakanin ƙabilun ƙasar ba, a dai dai lokacin da ake jajiberin gudanar da zaɓe. Wani mai suna Sebastian ɗan asalin jamhuriyyar Bene, wanda a yanzu ke sansanin baƙin haure kimanin 500 da 'yan ƙabilar Tubawa suka jibge a yankin Marzuq dake kudancin ƙasar ya koka game da matsanancin halin da suke ciki:

"Ya ce ni na zo nan Libiya ne domin inyi aiki . Ina da iyalina, amma a yanzu ba su san inda nake ba. Ba su sani ba ko ina raye ko kuma na mutu. Da wannan azabar da suke gana mana, gara su maido mu ƙasar mu ta asali."

Arbeitslose afrikanische Männer sitzen auf einer Mauer, Germa, Libyen
Yan ƙasashen Afirka da suka maƙale a LibiyaHoto: picture-alliance/dpa

Canma a Benghazi dake gabashin ƙasar ta Libiya labarin guda ne domin kuwa zanga-zangar nuna adawa da rabon wakilan ne ta gudana a ofishin hukumar zaɓen dake birnin, a yayin da a birnin Ajdabiyya kuwa wasu ɓata-gari suka ƙona kayayyakin zaɓen. Hukumar zaɓen Libiyar dai ta warewa yankin yammacin Libiya da ya haɗar birnin Tripoli kujeru 106, yayin da gabashin ƙasar daya haɗar da birnin Benghazi kuwa ya sami kujeru 60 kana yankin kudancin ƙasar ke da kujerun majalisa 34.

Ƙwararru dai na da ra'ayin cewar da wuya a san jam'iyyun da za su taka rawar gani a zaɓen majalisar da ta ƙunshi wakilai 120 da al'umma za ta zaɓa kai tsaye, da kuma wasu 80 da za'a fitar cikin jerin sunayen 'yan takarar da jam'iyyun suka gabatar.

Mawallafa: Nader Alsarras/ Saleh Umar Saleh

Edita: Usman Shehu Usman