Harkokin sufuri sun tsaya cak a Jamus
March 27, 2023Yajin aikin na wannan lokacin da aka dade ba a ga irinsa ba cikin gomman shekaru, ya haifar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da jiragen kasa da na ruwa da kuma motocin safa a wasu daga cikin jihohin kasar.
Gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar sun ce, yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara tattaunawa a karo na uku tsakaninsu da gwamnatin kasar. Alkalumma sun nuna cewa yajin aikin zai shafi kimanin fasinjoji dubu 400 da suka shirya yin balaguro a wannan Litinin din yayin da aka soke tashin da saukar jiragen sama a mafi yawancin filayen jirgen saman kasar.
Har wa yau, yajin aikin zai dakatar da jigilar kayayyaki da kuma fasinjoji a manyan tasoshin jiragen ruwa. Ana dai sa ran zama kan taburin tattaunawa tsakanin bangarorin a cikin wannan makon.