1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a Libiya ya janyo mutuwar mutane da dama.

May 14, 2013

Mutane aƙalla guda 15 aka ba da rahoton sun rasa rayukansu a sakamakon harin ƙunar baƙin wake da aka kai a kusa da wani Asibiti da ke a birnin Benghazi.

https://p.dw.com/p/18XE4
People gather at the scene of a car bomb explosion outside a hospital in Benghazi May 13, 2013. At least three people were killed and 17 wounded on Monday when the bomb exploded, a doctor at the hospital said. A second doctor said only one of the bodies had arrived intact, making it difficult to immediately establish the number killed. REUTERS/Esam Al-Fetori (LIBYA - Tags: CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Yazuwa yanzu, a kwai rahotannin da ke cin karo da juna dangane da addadin mutane da lamarin ya rutsa da su.Tun farko mataimakin ministan cikin gida na ƙasar Abdallah ya ce mutane guda 15 suka mutu kana wasu 30 suka samu raunika.

Yayin da ministan kiwon lafiya ya ce mutane fuɗu ne kwai suka cikka sannan wasu shidda suka jikata. Ɗarruruwan matasa sun gudanar da zanga zanga domin neman ganin gwamnatin ta kwance ɗamara mayaƙan ƙungiyoyin sa kai waɗanda ake kyautata zaton cewar sune ke da alhakin kai hari. Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah Wadai da hare haren tare da jaddada goyon bayan ƙasashen duniyar ga gwamnatin wucin gadin.

Mawalafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh