Harin ƙunar baƙin wake a Afghanistan
September 8, 2006Talla
Wani dan kunar bakin wake a birnin Kabul yayi sanadiyar mutuwan mutane 13 kana ya jiwa wasu 17 rauni. Harin wanda aka kai wa jerin motocin Amurka ya auku ne kusa da ofishin jakadancin Amurkan kuma sojojin ´kasar su biyu na cikin wadanda suka rasa rayukan su. Kawo yanzu dai babu wani tabbaci akann yawan mutanen da harin ya rutsa da su, amma wasu rahotanni sun nuna cewar mutane 16 ne suka gamu da
ajalin su.
An kai wannan harin dai dai lokacin da janar janar na kungiyar tsaro ta NATO ke zaman tattauna yiwuwar aika karin jami’an tsaro zuwa Afghanistan a kasar Poland. James Appathurai kakakin kungiyar tsaro ya hakikance cewar suna fuskantar yawan hare hare na ‘yan taliban a Afghanistan.