Hare-haren ta´adanci a ƙasar Yamal
July 3, 2007Hukumomin ƙasar Yamal sun bayana yaƙar ƙungiyar Alqa´ida bil haƙi da gaskiya, a sakamakon harin da su ka zarge ta, da kaiwa jiya litinin, wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 yan assulin ƙasar Spain.
A wani jawabi da ya gabatar, shugaban ƙasar Yamal, Ali Abdalah Saleh, ya ce, jami´an tsaro na da cikkakun rahhotani masu tabbatar da cewa, Alqa´ida ke da alhakin kai wannan mumuna hari, sannan ƙungiyar na cikin shirin kitsa wasu sabin hare-haren.
A game da haka, gwamnatin ta ɗauki matakai ƙwaƙƙwara na riga kafi , tare da binciko dukkan masu hannu a cikin harin na jiya.
Shugaba ƙasar Yamal, ya alkawarta bada tukuicin dalla dubu fiye da 80 ,ga duk wanda ya bada cikkaken bayyani a game da maɓuyar wannan yan ta´ada da su ke nema ruwa jallo.