Habasha ta sha fama amma yanzu sai tarihi.
Gwagwarmayar juyin-juya halin 'yan Habasha ta yi sanadiyar kawar da tsarin kwaminisanci, saboda kasa ce da ke bijirewa manufofin kasashen waje sannan kuma harkokin addini yana da tasiri.
Bukatar samar da makamai
"Amirka ba ta taimaka wa Habasha ba, a lokacin da kasar Somaliya ke kaddamar da yaki a kasar, saboda haka ne kungiyar sojoji ta Derg suka koma hannun gwamnatin gurguzu," da ke cewar Abebe Hailu wanda dalibin shari'a ne da ke fafutukar kawo karshen shugabancin gurguzu. A shekarun 1960 daliban Habasha da suka yi karatu a kasashen yamma an dasa musu akidar gurguzu kamin su komo Habasha.
Boren yan akidar gurguzu a Afirka
Shugabannin Tarayyar Soviet sun yi imanin kasashen Afirka za su kasance kasashen da suka karbi siyasar jari hujja. Kasar Habasha tana zama kasar da ake shigar da motocin dakon man fetur.
Manufar 'yan juyin-juya hali
Habasha ta fuskanci 'yan ta'adda a Arewacinta a yayin neman ballewar kasar Eritiriya. Duk da yawan makamai, da karfin dakarun soji da tsaussauran akidar gurguzu na faranta ran birnin Mosko. Dakarun kasar Habasha sun ki amincewa da masu neman kawo sauyi, abin da ya kawo aka yi ta zubda jini.
Ta'addacin zubda jini
Mutum-mutimin mata uku da ke tsaye a wajen gidan tarihi na Marty Memorial Museum da ke kusa da tsohon dandalin juyin-juya hali na Meskel Square. A shekara ta 1976, yayin wani jawabi Mengistu ya fasa wata kwalba cike da jini, inda kuma da haka aka kaddamar da kamfen na murkushe masu adawa juyin-juya hali, abin da ya yi sanadiyar hallaka daruruwansu.
Kura kurai da aka maimaita
Gidan tarihin ya maimaita rade-radin gangamin dakarun Derg dan nuna rashin gamsuwa da bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban gurguzun na cika shekaru 80, a lokacin da yawancin 'yan Habasha suka dandana kudarsu a harkar noma a shekara ta 1984, wanda shi ke zama bikin juyin juya hali na 10.
Shekarar dandana azaba
“Abebe ya ce a shekarar da zai kammala jami'ar shari'a, an kama wasu abokan sa shida. A farkon shekarun 1976 zuwa karshen shekarun 1978, Habasha ta fada cikin mawuyacin hali tsakanin dakarun Derg da 'yan tawaye. Dakarun Derg na farautar kwararru da daliban jami'a. Suna wulakanta su suna musguna musu, cin zarafi ya zama ruwan dare.
Wadanda matsin Derg ya shafa
Akwai benayen kidan tarihi da dama da aka lika hotunan wasu da aka kashe a zamanin sojojin Derg. Yana daga cikin akidar Marxist-Lininst cewa idan kana adawa da ra'ayin sauran jama'a za'a bindige ka ne. Shugabannin soji sun yi amfani da wannan akidar dan martaba ta su akidojin, don ci gaba da samun karfin mulki.
Babban wanda ya kitsa ta'asar
Mengistu shi ne kadai jami'i a lokacin da Derg ya kafa mulki. To amma an bar Machiavelli-like a baya koda yake wasu sojoji sun gudanar da jerin gwagwaryar ingiza yunkurin zubda jini. A watan Mayu na shekara ta 1991 kamin 'yan ta'adda su cimma shiga Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha Mengistu ya tsere zuwa kasar Zimbabuwe. Har yanzu yana rayuwa a kasar.
Bacewar abinda ya faru?
Tsohon dandalin juyin-juya hali da a yanzu ya cika da hada hadar kasuwanci ganinn yadda Habasha ke habaka. A kan daben da Mengistu ya yi jawabai, a yanzu shi ne dab da mashigar birnin inda tsahar jirgin kasa ya ke. Kadan ne ya rage daga radadin da al'ummar suka sha a baya daga mulkin gurguzu. Wani mutum da aka kama a lokacin juyin-juya ya ce bai taba tunanin jin irin azabar da ya sheda ba.