1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 100 a Nepal

Binta Aliyu Zurmi
November 4, 2023

Wata mummunar girgizar kasa mai karfin maki 5.6 a ma'aunin Richta ta afku a wani yanki na 'yan rabbana ka wadatamu da ke da cinkoson al'umma na Jajarkot a kasar Nepal.

https://p.dw.com/p/4YOhS
Nepal | Erdbeben
Hoto: Nepal Army/REUTERS

Lamarin  ya auku ne a daren jiya Juma'a, wanda kuma ya yi sanadiyyar rayukan mutane sama da 132 a cewar sanarwar da hukumomi suka fidda.

An sami asarar rushewar gidaje da dama, tuni masu aikin ceto suka fara kokarin zakulo mutanen da ke da saurin numfashi da suka makale a baraguzan gini.

Hukumomin lafiya sun ce sama da mutane 100 ne suka sami munanann raunika kuma yanzu haka ke karbar kulawa likitoci a asibiti.

Kasar Indiya da ke da nisan kilomita 500 daga inda wannan ibtila'in ya auku ta sanar da jiyo girgizar kasar.

A shekarar  2015, mummunar girgizar kasa mai karfin maki 7.8 ta auku a kasar Nepal inda aka yi asarar rayukan mutane sama da 22,000, inda al'umma suka shiga wani mawuyacin hali.

Karin bayani: Ana fuskantar gwagwarmayar raba kayan agaji bayan girgizar kasa a Nepal