1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Girgizar kasa ta kashe mutane 120

October 7, 2023

Kimanin mutane 120 suka rasa rayukansu yayin da wasu daruruwa suka jikkata sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.3 da ta auku a Afghanistan.

https://p.dw.com/p/4XFOB
Mutane a wajen gidajensu a birnin Herat da girgizar kasa ta afkawa
Mutane a wajen gidajensu a birnin Herat da girgizar kasa ta afkawaHoto: AFP/Getty Images

Iftila'in ya auku ne a yammacin lardin Herat, wanda bai da tazara da iyakar kasar da Iran.

Babban daraktan kula da kiwon lafiya na lardin, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, kimanin mutum 1,000 ne suka jikkata; kuma akwai fargabar adadin wadanda suka mutu ya karu yayin da ake ci gaba da aikin ceto. Kana ya kara da cewa, iftila'in ya haifar da katsewar wutar lantarki a yankin.

Faya-fayan bidiyon da aka wallafa a kafafen sada zumunta na zamani sun nuna yadda daruruwan mutane suka fito wajen gidajensu da kuma wuraren aiki a birnin na Herat.