Girgiza ƙasa a Indonesia
May 30, 2006Ƙasashe da ƙungiyoyin bada agaji na dunia, na ci gaba da kai taimako ga al´umomin Indonesia da bala´in girgizar ƙasa ya rutsa da su.
Har yanzu, a na ci gaba da gano ƙarin mutanen da su ka rasa rayuka a cikin wannan bila´i.
Alƙalluman baya bayan nan, da gwamnati Jakarta ta bayar, sun ce rayuka a ƙalla 5.400, su ka salwanta a cikin wannan girgiza ƙasa.
Dubunan jama´a, da su ka rasa matusugunnai, sun share dare na 3 ,a cikin yanayi mai ban tausayi.
Assibitocin ƙasar sun cika maƙil, sannan ga babu issassun ma´aikata da magungunna.
Majalisar Ɗinkin Dunia, ta yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, su girka manyan assibitoci 3, cikin gaggawa, da kuma taimakon maggunguna.
Ƙarin al´ajabi, a yanzu haka, a na cikin zullumin abukuwar wata sabuwar girgiza ƙasa.