Finidi ya ce kungiyar Super Eagles za ta dawo da martabarta
June 8, 2024Goerge na wannan cika baki a bayan da Najeriya ta yi kunnen doki a wasan share fage da ta buda da kasar Afrika ta Kudu a birnin Uyo da ke kudancin kasar.
Karin bayani: Finidi ya zama sabon mai horar da Super Eagles
Najeriya ce ta biyar daga kasashen rukuni na uku wato Group C, inda take da maki 3 kacal a wasanni uku da ta buga, lamarin da ya sanya ta a wani hali na kila-wa-kala dangane da cancantar shiga gasar kwallon kafa ta duniya.A halin yanzu dai kasar Lesotho ce ke kan gaba a wannan rukunin da maki 5, inda ta dara kasashen Ruwanda da Benin da maki 1, yayin da kasar Afrika ta Kudu da za ta fuskanci Super Eagles a mataki na biyu ke da maki 4, sai kuma Zimbabwe da ke da maki 2.
Karin bayani: Cece-kuce kan raba gari da kochin Super Eagles Jose Peseiro
Finidi George dai ya karbi ragamar kungiyar ta Super Eagles tun bayan rashin nasarar da Najeriyar ta yi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka gudanar a kasar Côte d' Ivoire.