1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faɗa ya ɓarke a birnin Sirte na ƙasar Libiya

October 1, 2011

Dakaru masu biyyaya ga tsofan shugaban ƙasar Libiya Muammar Khaddafi da na hukumar riƙwan ƙwarya na gwabza ƙazamin faɗa a birnin Sirte.

https://p.dw.com/p/12kJi
Hoto: dapd

A cewar babban komandan rundunar kwamitin ƙoli na riƙwan ƙwarya a Libiya, dakarunsa sun yi nasarar kewaye birnin Sirte mahaifar tsofan shugaban ƙasa Muammar Khaddafi.

Sannan a yanzu haka suna ci gaba da ɓarin wuta tare da sojoji masu biyyaya ga tsofan shugaban.

Jami´in na soja ya ce saura ƙiris a murƙushe sojojin Khaddafi a garin na Sirte.

A ɗaya wajen, jami´an agaji na ƙasa da ƙasa, musamman na ƙungiyar Red Cross ko kuma Croix Rouge sun isa bakin birnin na Sirte inda suke ƙoƙarin ba da tallafi ga farar hula.

Ƙungiyar kare haƙƙoƙin bani Adama ta Human Rights Watch ta yi kira da babbar murya ga ɓangarorin masu gaba da juna su tsagaita wuta, domin kai agaji ga farar hula wanda ba su ci kasuwa ba runfuna ke faɗa masu.

Sannan ƙungiyar ta yi kira ga komitin riƙwan ƙwarya a Libiya, ya ɗauki matakan tabbatar da adalci a gidajen kurkuku inda dubunnan mutane ke gurfane ba tare da sanin lefin da su ka aikata ba, kuma babu bayani game da ranar da za a yi masu shari´a.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal