1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fata da kuma damuwa bayan zaɓe a Libiya

July 8, 2012

Murna ka iya komawa ciki idan zaɓen na Libiya ya kasa samar da kyakyawan yanayi na 'yanci da walwala ga 'yan ƙasar.

https://p.dw.com/p/15TmK
epa03299131 Libyans celebrate the vote in the National Congress elections at the corniche road (seaside road), in Benghazi, Libya, 07 July 2012. Voters headed to the polls across Libya on 07 July to elect a 200-seat National Congress, which will have legislative powers and appoint a new government, amid fears of violence and calls for boycott in eastern cities. Around 2.7 million Libyans have registered to vote to elect the assembly, consisting of 120 directly elected members and 80 contenders from party lists. EPA/AMEL PAIN +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Cikin gaggawa da ɗokin kaɗa ƙuri'a ta farko a rayuwar da yawa daga cikin 'yan ƙasar Libiya, ya kau. Domin har yanzu da yawa daga cikin  'yan ƙasar na cikin damuwa da rashin sanin tabbas dangane da abubuwan da za su biyo bayan zaɓen na ranar Asabar da ta gabata.

Maimakon su hau kan tituna su yi ta murna kamar sauran takwarorinsu matasa, Meftah Lahwel ɗalibi a fannin koyon aikin likita da abokansa sun keɓe ne a wani gidan shan gahawa suna shawartawa kan abin da za su iya don ciyar da ƙasarsu gaba, bayan zaɓen dake zama wani abin tarihi ga ƙasar ta Libiya. 

"Zaɓen wani mataki a cikin tattaki mai yawa. Ya zuwa yanzu zaɓen ne kaɗai muka gudanar, muna da babban aiki a gabanmu. Abin baƙin baƙin ciki muna fuskantar babban hatsarin faɗawa cikin wata ƙasa mai bin tsarin addini. Idan muka kasa bayyana ra'ayinmu yanzu, muka kasa yin wani abin kirki na kare haƙƙin ɗan Adam da tsarin demokraɗiyya, to murna za ta koma ciki."

Babban aikin girke demokraɗiyya

Meftah Lahwel ya ce da sauran aiki a gaba matuƙar ana son girke sahihiyar demokraɗiyya, sai dai ba za su yi ƙasa a guiwa ba.

Da yawa daga cikin 'yan Libiya sun kwatanta zaɓen da wani bikin aure, inda suka fita ƙwansu da kwarkwatansu don sauke wannan nauyi, yayin da jami'an zaɓe suka rarraba ruwan sha da alawa da sauran kayan zaƙi don ƙarfafa guiwar masu kaɗa ƙuri'a.

Wahltag in Tripolis 07.07.2012 Kopierechte: Essam Zuber, DW Korrespondent in Libyen. Zugestellt von Moncef Slimi
Hoto: DW/E.Zuber

Hatta ƙwararrun masu sanya ido a zaɓe na ƙungyiar tarayyar Turai sun yi mamakin irin ɗoki da murnar dake tattare da 'yan ƙasar saboda zaɓen, dake zama babbar nasara ga da yawa daga cikin matasan ƙasar waɗanda suka ba da gagarumar gudunmawa a boren da ya kai ga kifar da gwamnatin marigayi Muammar Ghaddafi. Wasef Salem Albdrani yayi kyakkyawan fatan cewa kwalliya za ta biya kuɗin sabulu.

"Ina fata za su yi wani abin kirkiki domin ƙasarmu ta samu ci-gaba wajen kafa kyakkyawan mulkin demokraɗiyya, ba kamar sauran ƙasashen Labarawa ba inda har yanzu ake aiki da wani kundin tsarin mulki na gargajiya."

Fargabar komawa gidan jiya

Dubi da halin da ake ciki a ƙasashen Masar da Tunisiya waɗannan mutanen biyu wato Meftah Lahwel da Wasef Salam Albdrani na fargabar cewa Libiya ka iya komawa gidan jiya bayan ci gaban da ta samu na juyin juya hali.

An anti-election protester (C), who was shouting anti-election slogans, fights with pro-election residents in central Benghazi July 7, 2012. Crowds of joyful Libyans, some with tears in their eyes, parted with the legacy of Muammar Gaddafi on Saturday as they voted in the first free national election in 60 years. But in the eastern city of Benghazi, cradle of last year's uprising and now seeking more autonomy from the interim government, protesters stormed polling stations and burned hundreds of ballot papers. REUTERS/Youssef Boudlal (LIBYA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS ELECTIONS)
Hoto: Reuters

Dole kowane ɗan ƙasar ya ba da tasa gudunmawa wajen gina wata al'umma mai adalci da gaskiya da mutunta haƙƙin ɗan Adam muddin ana son ƙasar ta kasance a kan kyakkyawar turba.

Ganin cewa Libiya za ta kafa wani sabon tsarin siyasa gaba ɗaya, bayan sama da shekaru 40 ƙarƙashin mulkin Ghaddafi, matasan biyu sun ce wannan babbar dama ce da ba za su yarda ta kuɓuce musu ba.

Mawallafa: Karin Kails / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tano Bala

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani