1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Faransa da Jamus da Burtaniya na son a dakatar da yakin Gaza

August 12, 2024

Gwamnatocin Faransa da Jamus gami da Burtaniya, sun goyi bayan sabuwar aniyar sa jiki daga kasashen da ke shiga tsakani, don ganin an kawo karshen yaki a tsaknain Isra'ila da kungiyar Hamas a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4jOTB
Yanayin da ake ciki na jinkai a Zirin Gaza
Yanayin da ake ciki na jinkai a Zirin GazaHoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images

Kasashen na Turai dai sun nuna bukatar kasashen Amurka da Masar da ma Qatar, su daage wajen ganin an cimma tsagaita wuta, ta yadda za a sako wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su - da ma samun shigar da kayyakin jinkai a Zirin Gaza.

Sanarwar da ke da nasaba da wannan bukata dai, ta samu sa hannun Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da kuma Firaminista Kier Starmer na kasar Burtaniya.

Masu shiga tsakanin sun kwashe watanni suna kokarin bangarori masu yaki da juna sun amince da yarjejeniyar da za ta ba da damar samun daidaito a tsakani.

A ranar Alhamis da ke tafe ne dai ake sa ran komawa zaman tattaunawa domin ganin yadda za a cimma yiwurar dakatar da kai hare-hare a yankin falasdinu.