Fafutukar hamɓarar da gwamnatin Thailand
March 16, 2010Masu zanga - zangar nuna adawa da gwamnatin ƙasar Thailand, suna ci gaba da yin jerin gwano a Bangkok, babban birnin ƙasar, inda a wannan karon, suke bayar da gudummuwar jininsu, domin zubar dashi a hanyoyin shigowa ofisoshin hukumomin ƙasar - a fafutukar da suke yi ta neman gwamnatin ta amsa kiran da suka yi na gudanar da sabbin zaɓuka - a yanzu. 'Yan adawar dai, na son samar da jinin da yawansa yakai Lita 1,000 ne, wanda suke shirin zubawa a babbar ƙofar shigowa gidan gwamnatin ƙasar da misalin ƙarfe 6 na yamma - agogon ƙasar, wato 11 na dare kenan agogon GMT . Masu jerin gwanon, waɗanda kuma aka sani da ma'abota ja'ja'yen riguna, magoyon bayan tsohon Frime Ministan ƙasar Thaksin Shinawatra ne wanda aka hamɓarar da shi a wani juyin mulkin shekara ta 2006. Suna zargin cewar, gwamnatin bata bi doka ba wajen ɗarewa kan mulki, saboda hakane - a cewarsu, ta sauka daga mulki kuma ta kira sabon zaɓe, ba tare da wani ɓata lokaci ba. Fiye da mutane dubu 100 ne dai ke halartar zanga zangar a babban birnin ƙasar ta Thailand, wadda suka faro tun a ranar jumma'ar data gabata, kuma suka nemi Frime Ministan ƙasar dake mulki yanzu Abhisit Vejjajiva da ya rusa majalisar dokokin ƙasar.
A jawabin da Frime Ministan ya yi ta gidajen rediyo da telebijin, ya bayyana cewar, gwamnati ba zata iya biyan bukatun masu zanga-zangar ba a yanzu, domin kuwa waɗanda basu shiga cikinta ba ma suna alhakin gwamnati ta mutunta ra'ayinsu. Ya ƙara da cewar, za'a rusa majalisar dokoki ne kawai - idan har matakin zai kawowa ƙasar ci gaba.
A halin da ake ci kuma, wani jami'i a majalisar dokokin ƙasar, ya bayar da sanarwar ɗage zaman majalisar - a yau talata, kasancewar da dama daga cikin mambobin majalisar basu halarci zama ba, domin kare lafiyarsu.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Yahouza Sadisou