1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta kara wa Rasha tsauraran takunkumi

Abdullahi Tanko Bala
September 22, 2022

Kungiyar Tarayyar Turai ta kudiri aniyar sanya wa Rasha wasu sabbin takunkumi saboda yunkurin da take yi na mayar da wasu yankunan Ukraine cikin kasarta.

https://p.dw.com/p/4HE9l
Frankreich | Ursula von der Leyen im Straßburger Europaparlament
Hoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

Matakin kakaba wa Rasha sabbin takunkumin dai bai sami amincewar dukkanin kasashen kungiyar EU ba saboda suna gani  zai Sai cutar da tattalin arzikin kasashensu.

Kungiyar mai mambobin kasashe 27 a baya ta sanya wa Rasha jerin takunkumi har guda shidda tun bayan da shugaba Vladimir Putin ya umarci sojojinsa su afkawa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Bankuna da kamfanoni da kasuwanni har ma da fannin makamashi na jin radadin takunkumin yayin da aka kwace kadarorin jami'ai kimanin 1,200 ko kuma aka hana musu tafiye tafiye zuwa wasu kasashe.

Shugaban kasar Hungary Viktor Orban ya yi kiran a dage takunkumin da kungiyar tarayyar Turai ta sanya wa Rasha yana mai cewa yin hakan shi ne zai sa kasashen su farfado su kuma kauce wa fadawa matsalar koma bayan tattalin arziki.