1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar hana tsaffin jami'an gwamnatin Gaddafi sake rike mukami

May 5, 2013

Majalisar dokokin kasar Libiya ta kada kuri'ar haramta wa duk wanda ya rike babban mukamin gwamnati karkashin mulkin shekaru 42 na Marigayi Mu'ammar Gaddafi sake rike wani mukami.

https://p.dw.com/p/18SbW
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar dokokin kasar Libiya ta kada kuri'ar haramta wa duk wanda ya rike babban mukamin gwamnati karkashin mulkin shekaru 42 na Marigayi Mu'ammar Gaddafi sake rike wani mukamin gwamnati a cikin kasar.

Babu tabbas kan wadanda matakin zai shafa, saboda Firaministan kasar na yanzu Ali Zeidan ya rike mukamin jami'in diplomasiya, kafin ya koma bangaren 'yan adawa a shekarar 1980. Yayin da shugaban majalisar dokokin kasar Mohammed Magarief ke zama tsohon jakada, kafin ficewa daga gwamnatin ta Gaddafi a shekarun 1980.

'Yan bindiga sun kwashe fiye da mako guda wajen kawanya ga ma'aikatun harkokin wajen da na Shari'a, saboda neman ganin an kafa wannan ayar doka da ke kawar da tsaffin mambobin gwamnatin Marigayi Gaddafi daga sake rike mukami. Amma jami'an diplomasiyan kasashen duniya sun nuna damuwa, bisa yadda aka kada kuri'ar karkashin matsin lamba, wanda ya saba hanyar demokradiyya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal