1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Turkiya da Libiya

July 14, 2011

Gwamnatin ƙasar Turkiya ta yanke hulɗa jakadanci tsakanin ta gwamnatin Shugaba Ghaddafi tare da amincewa da ɓangaren 'yan tawaye, tare da ƙoƙarin baiwa ɓangaren na 'yan tawayen cikkakken goyon baya don cimma buƙatunsu

https://p.dw.com/p/11vTU
Ministan harkokin wajen Turkiya Ahmet Davutoglu a lokacin ziyararsa ga BenghaziHoto: AP

A juma'ar nan ce dai gwamnatin ta Turkiya za ta gudanar da wani taro game da ƙasar ta Libya wadda ake sa ran ministocin harkokin wajen na ƙasashen da ke ƙungiyar tsaro ta NATO za su hallarta da ma dai na sauran ƙasashe domin tattaunawa da 'yan tawaye game da makomar ƙasar bayan an kawar da gwamnatin shugaba Ghaddafi.

Wannan taron da ƙasar ta Turkiya za ta karɓi baƙunci dai wata 'yar manuniya ce da ke nuna ƙarfin ikon da ƙasar ke ƙoƙarin samu game da halin da ake ciki a ƙasar ta Libya a halin yanzu da ma dai nan gaba.

A saboda wannan yunƙurin da su ke yi ne ya sa su ka baje kolin tsare-tsaren da su ke ƙoƙarin bi wajen cimma manufarsu kamar dai yadda Selim Yenel ya bayyana.

"Tsarin da Turkiya ta ke da shi a bayyane ya ke. Wasu daga cikin abubuwan da za mu tattauna a taron da za mu yi shi ne halin da ake ciki a ƙasar da abin da zai biyo baya bayan da shugaba Ghaddafi ya kau daga karagar mulki da ma da batun baiwa 'yan tawayen ƙasar agaji na kuɗi."

Libyen Rebellen Mokhtar Milad Fernana
Madugun 'yan tawayen yammacin Libiya Mokhtar Milad

Tuni dai ministan harkokin wajen ƙasar ta Turkiya Ahmed Davutoglu ya ziyarci Bengahazi da ma dai sauran yankunan da 'yan tawayen ke iko da su da nufin ganin an kawo ƙarshen kiki-kaka ɗin da ake fama da shi tsakanin ɓangaren da ba sa ga maciji da juna kafin fara azumin watan Ramadan.

Baya ga wannan ƙasar ta Turkiya na ƙoƙarin ganin an samu sararin kai agaji ga waɗanda tashin hankalin ƙasar ya ɗaiɗaita.

A baya dai ƙasashe da dama sun ga baiken ƙasar ta Turkiya na ƙin ɗaukar mataki tun da wuri sai dai tsohon jakadan ƙasar ta Turkiya a Libya Uluc Özülker ya ce irin dangantakar da ke akwai tsakanin ƙashen biyu musamman ma dai ta ɓangaren tattalin arziki da kuma rashin tabbas game da yadda dambarwar za ta kaya.

"Lokacin da aka fara tashin hankali, ya zamewa Turkiya dole ta kare al'ummar ƙasarta da ke aiki a Libya. Dole ne ƙasar ta kwashe al'ummarta a ƙasar ta Libya. Abu na biyu shi ne masaniya da Turkiya ta ke da shi game da irin ƙarfin da Ghaddafi ke da shi. Abu na uku kuma irin kyakkyawar dangantakar da ke akwai tsakanin ƙashen biyu domin kuwa dukaknninmu 'yan uwan juna ne. Waɗannan abubuwa ne su ka sanya dole ƙasar ta zuba ido kan lamarin domin ganin yadda za ta kaya."

To duk da cewar warware matsalar ta Libya ba abu ne mai sauƙi ba, mahunta a ƙasar Turkiya na ganin yunƙurinsu na ƙulla ƙawance tsakanin su da ɓangaren 'yan tawaye zai taimaka wajen magance mastalar kamar dai yadda Uluc Özülker ya bayyana.

"Nan kusa ko kuma zuwa nan gaba Libya za ta fita daga cikin matsalar da samu kanta a ciki, ta bangaren sake gina ƙasar kuwa kamfanonin Turkiya za su cigaba da ikinsu saboda yadda tsakaninsu ya ke da ƙasar ta Libya amma dai ta bangaren fasaha da kuma kere-kere kuwa, kamfanonin na Turkiya za su samu babban ƙalubale saboda irin ƙarfin da ƙasashe kamar Amurka da Faransa da Burtaniya ke da su. Amma dai ta bangaren tattalin arziƙi da siyasa kuwa mastayin da Turkiya ta ɗauka ya yi daidai."


Mawallafi: Ayhan Sinsek/Ahmed Salisu

Edita: Ahmad Tijani Lawal