Masu salon magana na cewa soyayya ruwan zuma. Soyayya kan iya sace zuciyar dan Adam ba tare da ya yi la’akari da kankanta ko girman mutumin da aka zurfafa a cikin kogin soyayyarsa ba. A cikin shirin za a ji yadda wata matashiya a kasar Ghana ta tsinci kanta cikin soyayya da malaminta