1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun 'yan tawayen Libiya sun ce haƙon su ya kusa cimma ruwa

September 5, 2011

Sojojin na gwamnatin wucin gadin Libiya sun cigaba da ɗammarar kai hari a ɗaya daga cikin sansanonin da ke rufawa gwamnatin da aka hamɓarar baya

https://p.dw.com/p/12TUe
'yan tawaye a Bani walidHoto: dapd

Dakarun sun ce mai yiwuwa Gaddafi yana ɓoyewa a garin Bani Walid wadda ke kudu maso gabashin Tripoli. Yunƙurin tattaunawar da aka yi a yau litinin domin cimma yarjejeniyar miƙa wuyar garin ya ci tura, ko da ya ke, sojojin sun ce a shirye suke su tattauna. Ahmad Bani shine kakakin sojojin gwamnatin wucin gadin na Libiya

"Kwanaki uku ko hudu da suka wuce, akwai begen cewa garin Bani Walid zai sami 'yanci ba tare da an yi wani yaƙi ko rigima ba amma sun ƙi amincewa".

A halin da ake ciki kuma, ƙungiyar ƙawancen NATO ta cigaba da kai hari a wuraren da ake kyautata zaton Gaddafi yana da magoya baya, kamar mahaifarsa Sirte. Babban sakataren ƙungiyar Ansers Fogh Rasmussen ya ce ya tabbata an kusa kammala yaƙin na Libiya, ya kuma yaba da ayyukan da ƙungiyar ta gudanar tsakanin watanni shiddan da suka gabata yana mai cewa babu hare-haren da aka kai ta sama a tarihin irin waɗannan yaƙe-yaƙen kuma aka ci nasarar kare fararen hula kamar wannan.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu