Coronavirus: Duniya cikin alhini
March 26, 2020Da fari dai cutar ta Coronavirus ko kuma COVID-19, ta bulla ne a kasar Chaina, kafin daga bisani sannu a hankali ta mamaye duniya baki daya. An yi gargadin cewa idan ba a dauki matakan kariya cikin gaggawa ba, cutar za ta yi gagarumar illa a duniya baki daya, ganin cewa har kawo yanzu ba ta da magani.
Wanna dai ya sanya firgici cikin zukatan al'umma, musamman a kasashe masu tasowa, da suke fama da dinbim talauci da halin rashin tabbas musamman a bangaren kiwon lafiya. Kasashen Afirka na daga cikin kasashen da ke fama da talauci da matsala a fannin kula da lafiyar al'umma, kuma kawo yanzu kasashe kalilan ne cutar ba ta isa ba a nahiyar.
Kawo yanzu dai cutar ta halaka mutane sama da dubu 22 a fadin duniya baki daya, yayin da wasu dubbai ke kwance a asibitoci suna fama, baya ga wasu masu tarin yawa da suka warke daga cutar.