Buhari ya nemi karin hutu don duba lafiyarsa
February 5, 2017Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dokokin kasar ta kara masa hutu domin duba lafiyarsa a cewar wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar.
Sanarwar ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya aike da takarda ga majalisar dokoki a yau Lahadi 5 ga watan Fabrairu 2017 yana sanar da bukatar tsawaita hutunsa domin kammala wasu gwaje gwajen lafiya da likitoci suka bada shawarar a yi masa.
Tun farko shugaban ya dauki hutun makonni biyu domin duba lafiyarsa a Birtaniya.
Karin lokacin da shugaba Buharin ya nema dai ka iya yin tasiri akan amannar da ake da ita akan gwamnatinsa a daidai lokacin da ta ke fuskantar suka kan tsadar rayuwa da kuma yadda gwamnatin ke tafiyar da lamuranta.
Shugaban ya shirya komawa gida ne a yammacin yau to amma likitoci suka bashi shawarar jinkirtawa domin kammala gwaje gwajen lafiyar.