Brown zai yi murabus
May 11, 2010Firayim minista Gordon Brown ya sanar da yin murabus ɗin ne, domin bada damar kafa gwamnatin haɗaka da jam'iyar Liberal Demokirat ta masu sassaucin ra'ayi. Ci gaba da kasancewar Brown a kan shugabancin jam'iyar, abune da ake ganin zai iya kawo tarnaƙi a ƙoƙarin da Jam'iyar sa ta Labour ke yi, na samun goyon bayan jam'iyar Liberal Demokrat. Wannan mataki da Firayim ministan ya ɗauka, ana ganin ya sanya jam'iyar Conservative cikin wani hali na kota amince ta kulla ƙawance da Liberals, domin kafa gwamnati, ko kuma ta ci gaba da zama jam'iyar adawa. Tuni dai jam'iyar ta Conservative ta ce za ta duba buƙatun Liberals Demokrat, waɗan da suka haɗa da batun yin gyara a dokar zaɓen ƙasar ta Birtaniya. zaɓen da mutane da dama suka yi kukan cewa basu samu daman kaɗa ƙuri'u ba.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu