Barazanar yaɗuwar cututtuka a Nepal
April 30, 2015Talla
Jama'ar da suka tsira da rayukansu a girgiza ƙasar da ta auku a Nepal waɗanda ke yashe a waje cikin ruwa da iska.Na cikin fargaba jin tsoron yaɗuwar cututtuka kamar Kwalara da sauransu.
Ƙwararru sun yi gargaɗi cewar a irin yanayin da ake cikinsa,jama'a na iya kamuwa da cututtuka ta hanyar shan ruwan da ba shi da tsabta.Wanda kuma ka iya zama irin halin da Haiti ta samu kanta a ciki a sheraru 2010 bayan girgiza ƙasar da aka yi a can.