1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aski ya zo gaban goshi a kan ficewar Birtaniya daga EU

December 6, 2020

Babban mai shiga tsakani na Birtaniya a shirin ficewar kasar daga Tarayyar Turai, David Frost, zai gana da takwarorinsa na kasashen na EU nan gaba da yammacin wannan Lahadin.

https://p.dw.com/p/3mI9N
Belgien Brüssel | Brexit | Handelsabkommen
Hoto: Reuters/O. Hoslet

Dukkanin bangarorin za su yi kokari ne na yanke shawara dangane da yiwuwar cimma yarjejeniya ko kuma Birtaniya ta fice ba tare da wata yarjejeniyar ba.  

Zaman na yau shi ne ake ganin zai kasance na karshe, bayan tsawon lokaci da suka kwashe suna tafkan turanci ba tare da samun maslaha ba.

Tun da fari dai Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya tattauana ta waya da shugabar hukumar Turai, Ursula von der Leyen, inda har yanzu kawuna ke rarrabe dangane da samun damar Turan ta rika kamun kifi a ruwayen Birtaniya.