1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Artabu da masu fafutikar kare muhalli a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
September 17, 2018

An sake kama masu zanga-zanga 14 a ranar Lahadi bayan taho mu gama da jami'an tsaro a wani yanki da ake kokarin kafa kamfanin makamashi a yammacin Jamus.

https://p.dw.com/p/34zeZ
Weitere Entwicklung im Hambacher Forst
Hoto: picture alliance/dpa/C. Gateau

Wannan yankin dai da aka gabza da jami'an tsaro da masu fafutikar kare muhalli, ana so a kawar da wani daji ne kafin fara hakar ma'adanin kwal. Fiye da masu zanga-zanga 4,000 ne dai suka shiga gangamin na ranar Lahadi a dajin na Hambacher. Akwai kuma mutane takwas da 'yan sanda uku da suka samu raunika a cewar jami'an 'yan sanda.

Wadanda suka hada gangamin dai na cewa kimanin mutane 5,000 zuwa 9,000 ne suka halarci gangamin, kuma lamarin ya kazanta ne lokacin da kimanin masu zanga-zanga 200 suka yi yunkuri suka danna shinge na 'yan sanda a kokari na shiga dajin.

Tun ma dai a ranar Alhamis ake ta ba ta kashi da 'yan sandan lokacin da suka shiga aikin kawar da dakuna na wucin gadi da 'yan fafutikar kare muhallin suka kakkafa a cikin dajin a kokarin da suka yi kimanin shekaru shida suna yi na ganin ba a tashi gandun dajin na Hambacher ba.