1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana shirin zabo shugaban kasa a Sri Lanka

July 12, 2022

Bayan boren da ya kai shugabannin gwamnatin Sri Lanka ga sanar da ajiye aiki, majalisar dokokin kasar ta ce za su zabi sabon shugaban kasa cikin kwanaki da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4E2b3
Sri Lanka | Proteste gegen die Regierung
Hoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

'Yan majalisar dokokin kasar Sri Lanka sun amince da batun zaben sabon shugaban kasa a makon gobe, sai dai sun tafka turanci a kan wadanda za a zaben domin jagorantar gwamnatin.

Babban dai batun da ya fi daukar hankali a zamansu na yau Talata, shi ne mutanen da za su iya tsamo kasar daga tarnaki na tattalin arziki da da ma tabarbarewar lamuran siyasa da ta shiga.

Sakamakon kokawa da tsananin karancin abinci da makamashi da ma magunguna da 'yan kasar suke yi, wasu fusattun 'yan Sri Lankan suka afka wa gidan Shugaba Gotabaya Rajapaksa da ma na Firaministan kasar a karhsen mako.

Karfi da ma tsananin boren da jami'an suka gani, sun sanya su amincewa da ajiye aiki daga bisani.