Ana gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokokin Libiya
June 25, 2014Talla
A wannan Laraba 'yan ƙasar Libiya ke gudanar da zaɓen 'yan majalisar dokoki. Yayin zaɓen za a zabi 'yan majalisa 200 da za su maye gurbin majalisar dokoki ta wucin gadi da aka zaɓa a shekara ta 2012. An ware wa mata kujeru 32 daga ciki.
Ana fatan zaben zai kawo ƙarshen taƙaddamar siyasa da zaman tankiya da ƙasar ta samu kanta a ciki, shekaru uku bayan juyin-juya halin da ya kawo ƙarshen gwamnatin Marigayi Mu'ammmar Gaddafi. Ƙasar ta Libiya da ke yankin arewacin Afirka tana cikin ƙasashen duniya masu arzikin man fetur.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane