An zargi mayaƙan sa kai na Libiya da laifin cin zarafin bil adama
October 30, 2014Talla
A cikin wani rahoto da ta bayyana ƙungiyar ta zargi ƙungiyoyin mayaƙan daban-daban da aikata kisan gila a kan farar hula makonnin da dama da suka wucce.
Sannan kuma ta ce mayaƙan da ke faɗa tsakaninsu na harba rokoki da makaman atilare a anguwannin da ke cike da jama'a,waɗanda ke faɗawa a kan makarantu da asibitoci da kuma wasu gine-ginen gwamnatin.