An bukaci 'yan asalin kasar Iraki su koma gida
December 19, 2018Talla
Ministan harkokin wajen na Jamus Heiko Maas ya kuma kara da cewar duba da yadda harkokin tsaro suka inganta a Iraki, 'yan kasar masu zaman gudun hijira a Jamus za su iya komawa don ci gaba da rayuwa a kasarsu. Ministan ya baiyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata yayin da ya kai ziyara Iraki.
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan batu ministan harkokin wajen Iraki Mohammed Ali al-Hakim kira ya yi da 'yan asalin kasar da ke zaman gudun hijira a kasashe dabam-dabam na duniya da su dawo gida don ciyar da kasar gaba.