An ware kwanakin makoki a Muzambik
March 20, 2019Talla
Bayanai sun ce hanyoyin sadarwa sun sake dawowa a birnin Beira na kasar ta Muzambik, wanda ya fi fuskantar barnar da mahaukaciyar guguwa ta haddasaa 'yan kwanakin nan.
Kamfanin wayoyin sadarwa a kasar ya tabbatar da dawowar hanyoyin a wata sanarwar da ya wallafa ta shafukan sada zumunta.
Birnin na Beira dai na dauke ne da mutum akalla dubu 500, kuma a halin da ake mazauna yankunan da bala'in ya shafa na fama da tsananci kunci ne da kuma juyayi.
Sun kuma yi kiyasin akalla an rasa sama da mutum 200, kuma a farkon wannan makon ne Shugaba Filipe Nyusi na kasar, ya ce mutuwa ka iya shafar sama da mutum dubu guda.