1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu zanga-zanga a Myanmar

February 9, 2021

Jami'an tsaro sun harba harsashen roba da hayaki mai sa hawaye ga masu zanga-zangar nuna adawa da juyin mulkin da soji suka yi a kasar Myanmar.

https://p.dw.com/p/3p7Qm
Myanmar Proteste nach Militärputsch
Hoto: REUTERS

Masu zanga-zangar dai na son dawo da mulkin farar hula a kasar da ma neman sakin shugabar kasar Aung San Suu Kyi da ke tsare tare da wasu mukarabban gwamnatinta.

Tun a daren jiya ne dai shugabanin sojin da ke jagorantar kasar a yanzu suka bada sanarwar sanya dokar hana taruwar mutum fiye da 5 da kuma takaita zirga-zirga daga karfe 4 na safe zuwa 8 na dare a babban birnin kasar biyo bayan zanga-zangar da dubban mutane ke yi tun a ranar Asabar din da ta gabata.

Rahotanni na nuna cewa a wannan Talatar jami'an tsaro sun kama mutum a kalla 27 a birnin Mandalay na kasar.