1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sauke wasu jami'an gwamnatin Libiya

September 17, 2012

A wani matakin dai-daita al'amuran tsaro a kasar Libiya, hukumomin sun aiwatar da wani garanbawul a gwamnatin kasar

https://p.dw.com/p/16Agm
epa03370556 (FILE) A file phtograph dated 12 February 2012, shows Libyan interim Interior Minister Fawzi Abdelali speaking during a news conference in Tripoli, Libya. According to media reports on 26 August 2012, Abdelali resigned from his position after scathing criticism about security forces' handling of an upsurge of violence in the country. The resignation came shortly after an emergency meeting of the newly elected National Congress on security breakdowns in several areas of Libya. EPA/SABRI ELMHEDWI +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Ministan harakokin cikin gidan Libiya Fawzi Abdelali, ya sauke mukaddashin ministansa Wanis al Charef da shugaban hukumar tsaro ta kasa janar Hussein Bou Hamida. Wannan matakin ya biyo bayan harin da ya rutsa da jakadan kasar Amirka Chris Stevens da wasu jami'an ofishin jakadancin guda ukku a ran 12 ga watan nan. A cikin wata sanarwar da kanfanin dillanci labaran Faransa na AFP ya samu karantawa, ministan ya ce ya yi hakan ne domin kawo sauye-sauye a fannin tsaro na kasar.
Sanarwar ta ce an nada kanar Salahedine Dogman ya maye gurbin shugaban ma'aikatar tsaro ta kasar. Wannan na zuwa ne a dai-dai liokacin da kasashen musulmai a duniya ke zanga zangar nuna kyamar kasashen Yammaci, a dangane da wani mumunan fim din da ke walakanatar da manzon Allah Annabi Muhammadu.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Usman Shehu Usman