1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mahara sun kai wa masallaci a hari a Tillabery

August 21, 2021

Kimanin mutane 17 'yan bindiga suka halaka a sabon harin da gwamnati ta tabbatar da faruwarsa a wannan Asabar.

https://p.dw.com/p/3zJ7a
Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Gwamnan jihar Tillabery Ibrahim Tidjani ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Jamus, DPA, cewa maharan kan babura dauke da muggan makamai sun afka cikin masallacin kauyen Anzarou a yayin da mazauna ke tsaka da ibada, inda suka halaka mutane. 

Harin na kauyen  Anzarou da ke kan iyakar Nijar da Mali na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da mahara suka kashe mutane 37 ciki har da kananan yara a yankin na Tillabery da ke yammacin Jamhuriyar Nijar.