1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rusa majalisar 'yan tawayen Libiya

August 9, 2011

A wani abinda ke nuna alamun rashin jituwa tsakanin 'yan tawayen Libiya, shugabannin sun rusa majalisar zartaswa, inda aka kori man'yan jami'ai

https://p.dw.com/p/12DHe
Shugaban majalisar zartaswan Libiya, Moustafa Abdel JalilHoto: picture-alliance/dpa

'Yan tawayen ƙasar Libiya sun rusa kwamitin zartaswansu, a dai-dai lokacin da ake guna guni bisa rasuwar babban kwamandansu Abdull Fatah Yunis, wanda ba'a fayyace yadda ya rasu yayinda yake tsare a hannun 'yan tawayen. Shugaban kwamitin zataswan Mustafa Abdul Jalil ya kore man'yan jami'ai da yawa waɗanda suka haɗa da ministocin tsaro da na kudi da kuma ministan yaɗa labarai. Kwamitin zartasawan yan tawayen Libiya mai mutane 14, wadanda suka haɗa da mai kula da tsaro da ministan cikin gida, ana saran firai minista Mahmoud Jibril, zai naɗa wasu jami'ai a gaba. Kwamitin riƙon ƙorya ya shiga ruɗune bisa yadda suka tafiyar da mutuwar Janar Yunis, abinda ya kawo shakku bisa haɗin kan da 'yan tawayen ke da shi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar