1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gudanar da zaben majalisar dokoki a Italiya

Abdoulaye Mamane Amadou
July 21, 2022

Rikicin siyasa na kara daukar dumi a Italiya, bayan da firaminista Mario Draghi ya yi marabus shugaban kasa ya rusa majalisa ya kuma kira wani sabon zabe a watan Satunba

https://p.dw.com/p/4EUTU
Italien I Der italienische Ministerpräsident Mario Draghi im Parlament
Hoto: Andrew Medichini/AP/picture alliance

Shugaba Sergio Mattarella na Italiya ya rusa majalisar dokokin kasar jim kadan bayan karbar takardar marabus din firaminista Mario Draghi a wannan Alhamis.

Shugaba Mattarella ya ce ya dauki matakin rusa majalisar dokokin ne bayan da aka kasa samun jituwa kan tafiyar da gwamnati, a saboda haka nan da kwanaki 70 za a gudanar da sabon zaben 'yan majalisar domin kafa wata sabuwar gwamnatin"

Rahotanni sun ce za a gudanar da sabon zaben 'yan majalisar ne a ranar 25 ga watan Satumban wannan shekarar, bayan marabus din shugaban gwamnatin kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.

Mario Draghi wanda kawancen jam'iyyun da ke mulki suka juyawa baya ya bayyana cewa "yana alfahari da aikin da ya yiwa gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaban kasa."