An kashe wani babban jam'in tsaro a Libiya
August 12, 2014Talla
Kisan ya faru ne wannan Talatar(12.08.2014) inda wasu mutane masu fuskoki a rufe, suka buɗe wuta ga motar Kanal Mohamed al-Souissi.
Wanda ke kan hanyarsa ta dawowa gida daga birnin Tajoura da ke gabashin Tripoli, inda ya halarci zaman taron Majalisar wannan ƙaramar hukumar a cewar wata majiyar jami'an tsaro. Daraktan 'yan sandar ya rasu ne lokaci kaɗan bayan da aka isa da shi zuwa wani asibiti mafi kusa, kuma babu wasu da suka ɗauki alhakin kai wannan hari yazuwa yanzu
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane