1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha ta karbe iko da wani yanki kusa da Donetsk

Abdoulaye Mamane Amadou
March 12, 2024

An kai hari da jirgi maras matuki a ma'aikatar magajin garin yankin Belgorod na kasar Rasha mai iyaka da Ukraine a daidai lokacin da Rasha ke ikrarin karbe iko da wani yanki a Ukraine.

https://p.dw.com/p/4dQun
Hoto: Pavel Kolyadin/dpa/TASS/picture alliance

Gwamnan yankin ya sanar da cewa harin ya lalata wasu sassan ma'aikatar magajin garin Belgorod tare da raunata mutane biyu.

Wanann na zuwa a yayin da dakarun Rasha suka tabbatar da karbe iko da wani kauyen na gabashin Ukraine na kusa da Donetsk mai iyaka da Rasha.

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar a cikin wata sanarwa da cewar dakarunta sun shata layi a fagen daga a yankin Nevelské, bayan dauki ba dadi da abokan gaba a Ukraine.