1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira da dama sun hala a Libiya

Gazali Abdou Tasawa
July 3, 2019

A kasar Libiya 'yan gudun hijira kusan 40 ne suka halaka a cikin wani hari ta sama da aka kai a wata cibiyar da ake tsare da 'yan gudun hijira a kusa da birnin Tripoli.

https://p.dw.com/p/3LUTj
Libyen Luftangriff Tajoura Detention Center bei Tripolis
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito kakakin hukumomin agaji a birnin na Tripoli Osama Ali na cewa ko baya ga mutuwa akwai wasu 'yan gudun hijirar 70 da suka ji rauni a cikin harin da aka kai a cibiyar tasu mai kunshe da 'yan gudun hijira sama da 120. 

Tuni dai gwamantin Tripoli wacce Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita ta dora alhakin wannan kisa ga sojojin Khalifa Haftar wadanda yau da watanni uku suka kaddamar da wani gagarimin hari da nufin kwace iko da birnin na Tripoli. Ya zuwa yanzu dai babu wani bangaren da ya dauki alhakin kai wannan farmaki a cibiyar 'yan gudun hijirar.

 Sai dai kafafan yada labarai na kusa da Marechal Haftar sun tabbatar a jiya Talata da cewa an kai wasu jerin hare-hare ta sama a biranen Tripoli da unguwar Tajoura mai kunshe da barikoki da dama na sojin gwamnatin Tripoli wadanda ke yawan fuskantar hare-hare ta sama daga sojojin Haftar.