An fara zaɓen 'yan majalisa a Amirka
November 4, 2014An fara kaɗa ƙuri'u a kasar Amirka da nufin zaɓen 'yan majalisan wakilai na tarayya da na dattawa da ma na gwamnoni a wasu jihohin ƙasar. Jihohi shida ne suka fara buɗe runfunan zaɓen sakamakon banbancin lokacin da ke tsakanin sassa ƙasar ta Amirka, daga cikinsu kuwa har da Connecticut da New Jersey da New York da indiana da kuma Kentucky. Mutane miliyan 200 ne suka cancanci kaɗa ƙuri'a domin sabinta ɗaukacin kujerun majalisar wakilai, da kujerun dattawa 36 daga cikin 100, da kuma na gwamnoni 36.
Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar ta nunar da cewar jam'iyyar Republican za ta samun rinjaye a majalisar wakilai. Sannan kuma jam'iyyar Democrat ta su shugaban Barack Obama za ta iya shan kaye a majalisar dattawa. Idan ko hasashen ya tabbata, to dai Obama zai fuskanci ƙalubale wajen gudanar da harkokin mulki saboda turjiya da zai fuskanta da 'yan Republican da za su sami rinjaye a majalisun biyu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane