1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara shirin kafa sabuwar gwamnatin Libiya

October 15, 2012

Majalisar dokokin Libiya ta amince da Ali Zeidan a matsayin sabon fira ministan kasar.

https://p.dw.com/p/16Pyl
Hoto: AP

Sabon Fira ministan ƙasar Libya Ali Zeidan ya fara shirye shiryen kafa sabuwar gwamnati, kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Tsohon jami'in diplomasiyan yana cikin waɗanda su ka taka rawar kawar da gwamnatin Marigayi Mu'ammar Gaddafi cikin shekarar da ta gabata ta 2011.

Majalisar dokokin ƙasar ta Libya da ta zaɓi Ali Zeidan a matsayin sabon fira ministan ta bashi wa'adin makonni biyu ya gabatar da sunayen 'yan majalisar gudanarwa domin tantancewa.

Tilas majalisar dokokin ƙasar ta Libiya, ta amince da sabbin mambobin gwamnatin kafin su fara aiki, kuma ita ce majalisa da farko da aka zaɓa cikin ƙasar bisa tafarkin demokaraɗiyya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita Mohammad Nasiru Awal