1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta zargi Shell da gurɓata muhalli a Najeriya

August 3, 2012

Malalar man fetur a yankin Naija Delta na Tarrayar Najeriya, na da nasaba da rashin kulawa daga kamfanin Shell da ke yin aiki haƙar man a yakin

https://p.dw.com/p/15jGr
This undated photo shows a Shell Oil rig in the Niger Delta, Nigeria. Nigeria's latest hostage crisis came to a peaceful end Sunday, June 4, 2006, as six Britons, one American and one Canadian held captive for two days were released unharmed, looking tired, but in good health. A group of unidentified militants from southeastern Bayesla state who were demanding jobs and money kidnapped the expatriates Friday from an offshore oil platform operated by Dolphin Drilling Ltd. (AP Photo/Shell Oil)
Hoto: AP

Ƙungiyar kare hakin bil adama Amnesty International ta ce babbar kasawa ce kamfanin mai na shell ya yi, akan rashin bayar da sahihan baiyanai akan binciken da ya gudanar dangane da aikin hakar man da ya ke yi a yankin Naija Delta na Tarrayar Najeriya wanda ya janyo mumunar gurɓata muhali a wani ɓangaran na man fetir da ke tarara a cikin gonaki.

A cikin wata sanarwar da ta baiyana daraktar ƙungiyar Audrey Gauhran, ta ce abin takaici ne dangane da yadda kamfanin ya musunta cewar ba shi ne ke da alhakin malalar man ba a ƙauyen Bodo Greek a cikin watan Yuni da ya gabata.wanda ya lalata gonaki manoma kamar dubu 11 dake zaune a yankin wanda kuma daga bisani binciken kungiyar ya gano cewar bututun man, na shel sun yi tsatsa ne abinda ya hadasa tarrara man. Kamfanin dai na shell na zargin barayi masu fashin bututu domin satar man, da laifin hadasa lamarin.

Mawallafi : Abdourahaman Hassane
Edita Abullahi Tanko Bala