Ambaliyar ruwa a habasha tayi ta´adi da yawa
August 16, 2006Talla
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka dinga sharawa a kasar Habasha a watan nan yayi ajalin mutane a kalla 700.
Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya rawaito cewa wasu dubbannin mutanen kuma sun rasa gidajen kwanan su.
Ya zuwa yanzu dai ambaliyar ruwan a cewar jami´an bayar da agajin gaggawa na kawo cikas wajen gudanar da ayyukan su na ceto.
Bayanai dai sun shaidar cewa ambaliyar ruwan ta hana yin zirga zirga a tsakanin garuruwa da kauyuka da daman gaske a yankin da al´amarin ya faru.
Kasar ta Habasha data sha fama da matsalar fari a bara, a cikin yan makonnin nan kuma na fama ne da ambaliyar ruwan na sama.