Al'ummar Libiya ta ƙaddamar da zaɓe
July 7, 2012An buɗe runfunan zaɓe a Libiya domin gudanar da abun da ake sa ran zai zama zaɓe mafi sahihanci a ƙasar bayan shekaru 60.
Wato shekaru 40 na mulkin kama karyar marigayi Kanar Mu'ammar Gaddafi.
Waɗanda suka cancanci jefa ƙuri'ar masu yawan aƙalla milliyan uku, zasu zaɓi majalisa ce mai mambobi 200 wacce kuma zata zaɓi Frime Minista da Majalisar Ministoci, kafin daga bisani ta yi shinfidar gudanar da zaɓen 'yan Majalisar dokoki wanda ake kyautata zaton gudanarwa a badi idan Allah ya kaimu, bisa tanadin sabon kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda shima Majalisar zata ɗauki nauyin girkawa.
Abubakar Halloul wani ma'aikacin gidan rediyo ne a Libiyan wanda ke ɗokin gudanar da aikin jaridarsa cikin walwala a lokacin wannan zaɓe.
"Wannan ne karon farko da muke da damar yin aikinmu cikin walwala, zamu iya amfani da shiƙa-shiƙan demokradiyya ba tare da mun ɓoye wasu batutuwa ba, yanzu ma zan iya zantawa da jama'a a kan hanya, in basu damar bayyana ra'ayoyinsu in kuma sanya a rediyo yadda kowa da kowa zai ji ya kuma amfana"
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar