1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al'umar Kamaru na zaben shugaban kasa

October 8, 2018

Kamaru na zaben shugaban kasa, zaben da Paul Biya ke neman ci gaba da mulki. A halin da ake ciki jam'ian tsaro a Bamenda a yankin arewa maso yammaci sun harbe wasu mutane uku da ke yin harbe-harbe a kan jama'a.

https://p.dw.com/p/3679H
NO FLASH Wahl in Kamerun
Hoto: dapd

A wannan Lahadi al'umar kasar Kamaru ke zaben shugaban kasa, zaben da Shugaba mai ci Paul Biya ke neman ci gaba da jagoranci karo na bakwai. Manyan jam'iyyun MRC da FDP masu adawa sun kai ga hadewa daf da zaben, don ganin yadda za su karbe mulki daga hannun Shugaba Biya mai shekaru 85 a duniya. Kasar ta Kamaru na fama da rikice-rikice, musamman a yankinta da ke amfani da turancin Ingilishi, inda alkaluma ke cewa an rasa akalla rayukan fararen hula 420 da sojoji 175 yayin da su kuwa 'yan aware, bila adadin.

Ko a Juma'ar da ta gabata ma dai, an kashe wasu 'yan aware uku a birnin Buea da ke yankin kudu maso yammacin kasar, yankin da masu gwagwarmayar ballewa ke ikirarin sai sun kafa kasa.