1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai sauran rina a kaba a rikicn Libiya

June 15, 2013

Har yanzu tsugune ba ta kare ba a Libiya sama da shekara guda bayan da 'yan tawayen NTC suka kashe tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi,yayin juyin-juya halin kasar.

https://p.dw.com/p/18qPu
Hoto: Getty Images

Akalla dakarun sojojin Libya biyar ne suka rasa rayukansu yayin wata musayar wuta tsakanin jami'an tsaro na musamman da kuma 'yan bindiga a gabashin birnin Benghazi na waqnnan kasa. Jagoran riko na rundunar jami'an tsaron ta musamman Salem al-Konidi, yayi gargadin cewa, akwai yiwuwar a zubar da jini mai yawa a yankin biyo bayan wannan arangamar da sukayi da masu dauke da makaman, arangamar da ta zo mako guda bayan da rikici a yankin yayi sanadiyyar mutuwar mutane 30.

Tun da farko rundunar jamai'an tsaron ta musamman ta sanar da cewa jami'anta biyu sun jikkata yayin musayar wuta da 'yan bindiga a shafinta na Facebook, kafin da ga bisani ta sanar a shafin nata cewa dakarunta 3 sun rasa rayukansu a musayar wutar. Rahotanni sun bayyana cewa tun da misalin karfe hudu na asuba ne aka fara jin karar harbi da manyan bindigogi da kuma karar abubuwa masu fashewa a kusa da shalkwatar rundunar jami'an tsaron ta musamman da bata da tazara da cikin birnin na Benghgazi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe