1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan wakar batanci

Nasir Salisu Zango RGB
August 10, 2020

Wata babbar Kotun shari'ar musulunci da ke a Kano ta zartas da hukuncin kisa akan wani matashi mai suna Yahya Sharif Aminu da kotun ta samu da laifin yin sabo ta hanyar furta kalaman cin zarafi ga manzon Allah SAW. 

https://p.dw.com/p/3glFx
Symbolbild Selbstmord
Hoto: vkara - Fotolia.com

Baya ga mawaki Yahya Sharif da baitukansa suka jefa shi cikin matsala, kotun a karkashin mai shari'a Aliyu Muhammad Qani ta zartas da hukuncin daurin shekarun 10 da aikin wahala a gidan gyaran hali ga wani matashin mai suna Umar Faruk Bashir, wanda shi kuma kotun ta ce ta same shi da laifin shiga alfarmar ma'aiki wajen yin munanan kalamai ga mahaliccin.


Kafin zartas da hukunci dai, mai gabatar da kara Aminu Sani, ya karanta musu laifin da ake zargin sun aikata, kuma nan take suka amsa, Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da ke a arewacin Najeriyar, Isma'ila Na'abba Afakallah, wanda hukumarsa na daga cikin wadanda suka yi korafi ya ce irin wannan hukunci shi ne zai zama izina ga masu shirin aikata irin wannan sabo.