1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ƙasar Libiya ɓarin wuta ya mamaye Sirte

October 3, 2011

Mazauna birnin Sirte mahaifara kanal Gaddafi na cikin mummunan hali sakamakon ruwan rokoki tsakanin dakarun Gaddafi da na gwamnatin wucin gadi Libiya.

https://p.dw.com/p/12kxG
Wadanda yakin Sirte ya ritsa da suHoto: dapd

A ƙasar Libiya mazauna birnin Sirt na ci gaba da picewa sakamakon fadan da ake yi, tsakanin dakarun gwamnatin wucin gadi da magoya bayan Kanal Gaddafi. Ƙungiyar agajin gaggawa ta Red Cross ta yi gargaɗin cewa birnin Sirte na cikin tsananin buƙatar magunguna, inda ƙungiyar ta kwatanta lamarin da kasance wani mummunan yanayi. Wani jami'in ƙungiyar yace dakarun gwamnatin wucin gadi na cilla rokoki a kan asibitin birnin, a yunƙurin da suke yi na karɓe iko da Sirte. Shugaban gwamnatin wucin gadin ƙasar a jiya yace mazauna birnin Sirte suna da kwanaki biyu don picewa. Waɗanda ke tserewa daga birnin suka ce basu da labarin yarjejeniyar da aka yi, kuma ba a daina ɓarin wuta a birnin ba. Shugaban wucin gadin dai ya sha baiwa mazauna Sirte wa'adi da su pice da yin barazanar ƙaddamar da farmaki, tun a watan Augosta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Halima Balaraba Abbas