1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarshen mulkin kama karyar shekaru gommai a Libiya

August 22, 2011

Gwamnatin Muammar Gaddafi a Libiya tana dab da rugujewa, bayan da 'yan tawaye suka kame kuma suke iko da yankunan da yawa na babban birnin ƙasar wato Tripoli.

https://p.dw.com/p/12LIp
Hoto: dapd

Wannan wani albishir ne inji Rainer Sollich, shugaban sashen Larabci na Deutsche Welle a cikin sharhin da ya rubuta.

Alamar ƙarshen gwamnatin Muammar Gaddafi wata hujja ce ta farin ciki, domin wani mulkin kama karya na tsawon shekaru 42 zai kawo ƙarshe. 'Yan Libiya suna da 'yancin walwala da zaɓawa kansu abin da suke so. Suna da 'yancin kyakkyawar rayuwa ba tare da tsangwama ko tursasawa ba. Sun nuna ƙarfin zuciya da asarar rayuka a gwagwarmayar ƙwato wannan 'yanci.

Wannan nasarar soji da ba ta yiwu ba in ba don taimako daga ƙasashen yamma ba. Hare haren bama-bamai ta sama da NATO ta yi ta yi suka share musu fage. Amma hakan bai taƙaita nasarar sojin 'yan tawayen ba waɗanda ba su da ƙwarewa da kuma isassun makaman yaƙi.

Bürgerkrieg in Libyen Erfolg der Rebellen
Gaddadfi ya zama abin dariya a tsakanin 'yan LibiyaHoto: dapd

Jan aiki na gaban 'yan Libiya bayan Gaddafi

Wannan nasarar na tattare da wani nauyi mai girma, domin girke demokraɗiyya da mulkin farar hula a Libiya zai yi wuya fiye da a ƙasashen Tunisiya da Masar, kasancewa a ƙarƙashin Gaddafi babu jam'iyun siyasa da hukumomin gwamnati na zamani. Wato kenan yanzu ƙasar za ta fara tun daga tushe. Saboda haka ya kamata tarayyar Turai ta taimaka bisa manufa. A da ta yi fatan mahukuntan kama karya a Tripoli za su aiwatar da sauye sauye, inda hakan ya sa ta kawar da kai daga cin zarafin da ake wa al'umar Libiya.

Taimako daga Turai domin shimfiɗa kyakkyawan mulki

Sai dai babban nauyin yana kan 'yan Libiya ne kansu. Gwagwarmayarsu ta nuna cewa ana iya kawar da mulkin fir'aunanci da bakin bindiga. Hakan wani ƙarfafa guiwa ne ga 'yan adawa a Siriya, Yemen da sauran ƙasashe. Suna bore ne akan 'yanci iri ɗaya, saboda haka su ma sun cancanci tallafi daga Turai. Ya zama tilas 'yan Libiya su nuna wa duniya cewa a haɗe za su iya fasalta makomarsu da kansu, duk da mummunan saɓanin dake akwai tsakanin al'momin ƙasar. Dole ne a yi watsi da ɗaukar fansa akan magoya bayan tsohuwar gwamnati, domin haka wata guba ce ga sabuwar alƙibkar siyasar ƙasar. Dole dukkan 'yan adawa da suka rarrabu su haɗe kansu wuri guda. Dole a shigar tare da duba buƙatun dukkan ƙabilun ƙasar daidai wa daida. Ana buƙatar sabon kundin tsarin mulki sannan dole a yi kyakkyawan shiri na gudanar da zaɓen demokraɗiyya.

Bürgerkrieg in Libyen Erfolg der Rebellen
Hoto: dapd

Ko da yake duka waɗannan za su ɗauki lokaci kamar yadda ake gani a Masar, amma bai kamata su samar da sakamakon da ba za a so gani ba musamman a Turai, wato ƙarfafa tsattsauran ra'ayin Islama. Idan Turai ta samu nasarar tallafa wa shirin girke kyakkyawar demokraɗiyya a Libiya ba tare da yi ruwa da tsaki a harkokin siyasar ƙasar ba, to Libiya ka iya zama zakaran gwajin dafi ga haɗin kai tsakanin Turai da ƙasashen Larabawan yankin Tekun Bahar Rum. Kuma ko da yake a sane Jamus ta ƙi shiga cikin taron dangin soji akan Gaddafi, amma zai yi kyau idan ta taka rawa a haɗin kan siyasa da wannan ƙasa.

Mawallafa: Rainer Sollich / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai